A cikin wata sanarwar da ya fitar, al Arabi ya yi kira ga gwamnatin kasar Yemen da ta dakatar da nuna karfi kan masu zanaga-zangar lumana, kana ya bayyana cewar, mai yiyuwa ne ci gaba da nuna karfi ya janyo barazana ga makomar kasar da ma al'ummarta.
Al-Arabi ya yi marhabin da kudiri mai lamba 2014 na kwamitin sulhun MDD, kan kasar ta Yemen, wanda baki dayan kwamitin ya amincewa a ranar Juma'ar makon jiya, wanda ya bayyana yanayin matukar damuwa a Yemen. Kudirin dai ya bukaci dukkan bangarori su guji amfani da karfi don cimma muradinsu na siyasa.
Yarjejeniyar ta GCC da aka fara shirin samarwa tun cikin watan Afrilu, kana bangaren adawa na Yemen ya rattabawa hannu a cikin watan Mayu, ta nuna bukatar Shugaba Saleh ya bar gadon mulki cikin kwanaki 30 tare da mikawa mataimakinsa madafar iko, wanda shi kuma ake fatan ya kafa wata gwamnatin hadin kasa karkashin kulawar bangaren na adawa, sannan a shirya zabukan shugaban kasa cikin kwanaki 60.
A karo uku shugaba Saleh yana janyewa sanyawa yarjejeniyar hannu a daidai lokacin da ya kamata ya yi hakan. Sai dai a ranar Asabar da ta shude, gwamnatin ta Yemen ta ce, zata baiwa kudirin mai lamba 2014 kulawar da ta dace. (Garba)