Manzon musamman na M.D.D ya ce, ya sa ran alheri ga kokarin da jam'iyyu daban daban na kasar Yemen suke yi na daddale yarjejeniyar shimfida zaman lafiya
A ran 26 ga wata, manzon musamman na babban saketaren M.D.D mai kula da batun Yemen Jamal Omar ya gana da jadakan kasar Sin da ke kasar Liu Denglin, ya bayyana cewa, yana sa ran alheri ga kokarin da jam'iyyu daban daban na kasar Yemen suke yi na daddale yarjejeniyar zaman lafiya .
Jamal Omar ya bayyana wa Liu Denglin halin da ake ciki a yanzu dangane da shawarwarin da ke tsakanin jam'iyyar da ke kan karagar mulkin kasar da jam'iyyar adawa da gwamnati da sauran jam'iyyu daban daban. Ban da haka kuma, Jamal Omar ya bayyana cewa, zai bayyana wa kwamitin sulhu na M.D.D halin da kasar Yemen take ciki, kuma yana fatan za a warware rikicin kasar tun da wuri.(Abubakar)