in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya sabunta ka'idojin aiki da aka baiwa dakarun MDD a Abyei
2013-05-30 10:30:59 cri

A ranar Laraba, kwamitin sulhu na MDD ya kada kuri'ar kara tsawon lokacin aiki da aka baiwa dakarun MDD a Abyei (UNISFA), zuwa 30 ga watan nuwamban shekarar 2013, tare kuma da yin kira ga kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, su aiwatar da matakan kafa aminci tsakanin al'umomi daban daban dake yankin.

Kwamitin sulhu mai mambobi 15 ya yi tuni kan cewar, yarjejeniya da aka kulla ranar 20 ga watan Yunin shekarar 2011 ya gindaya cewa, kada kowa ya shigar da makamai yankin Abyei, illa dakarun UNISFA, bisa kuduri da kwamitin ya tsayar.

Hakazalika, kwamitin ya bukaci gwamnatocin kasashen biyu su dau dukkan matakai da suka dace don tabbatar da cewa, an kawar da fadace-fadace a yankin Abyei ko da ma za ta kai ga ajiye makamai ne baki daya.

A makon da ya biyo bayan kulla yarjejeniyar ne kwamitin sulhu ya kafa UNISFA, domin ganin yadda ake tafiyar da yarjejeniyar, kana da umurtar UNISFA da ta yi amfani da karfin soja wajen kare farar hula da masu aikin tallafawa bil-adama.

Aikin da aka baiwa dakarun na MDD karkashin jagorancin kasar Habasha a yankin na Abyei mai arzikin mai wanda kuma kasashen Sudan da Sudan ta Kudu ke takaddama a kai, zai kare ne a watan da muke ciki.

A cikin kudurin, kwamitin sulhun ya jadadda cewa, karin hadin kai tsakanin gwamnatocin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu yana da muhimmanci matuka ga zaman lafiya, tsaro da dorewa, da ma dangantaka ta nan gaba tsakanin kasashen biyu.

Kwamitin sulhun har wa yau ya yi kira ga gwamnatocin biyu su dau matakai ba tare da bata lokaci ba wajen kafa aminci tsakanin al'ummomi dake yankin Abyei, har ma da daukar matakan yin sulhu a yankunan karkara, in ji kudurin.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China