in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka 'yan tawaye sama da 70 a Kudancin Kordofan a Sudan
2013-05-27 09:56:57 cri

Wasu rahotannin baya bayan nan sun bayyana cewa, sojojin gwamnatin Sudan sun kai wani simame kan sansanonin kungiyar hadakar 'yan tawayen nan ta 'Revolutionary Front' a jihar Kudancin Kordofan, bayan da magoya bayan kungiyar suka farma yankin Al-Dandaro.

A cewar kakakin rundunar sojin gwamnati dake yankin Al-Sawarmy Khalid Saad, farmakin da suka kai ya haddasa kashe 'yan tawayen 70, yayin da kuma da dama suka tsere daga sansanonin da suka yi tinga. Saad ya kara da cewa, ana ci gaba da binciken dukkanin wuraren da maharan suke boye domin fatattakar su, duka dai da nufin maido da yanayin zaman lafiya da tsaro a yankin.

Jahohin Kudancin Kordofan da Blue Nile dai na shan fama, da dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun kungiyar SPLM reshen arewaci, tun daga shekarar 2011 da ta gabata, biyowa bayan samun 'yancin kan Sudan ta Kudu. Ko a watan Afirilun da ya gabata ma sai da rundunar gamayyar 'yan tawayen "Revolutionary Front Alliance", ta kai hare-hare a yankunan Um-Rawaba, da Abu-Karshula dake jihar Kudancin Kordofan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China