in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'ar MDD ta yi kira da a baiwa al'ummar Sudan da suka rasa muhalli karin taimako
2013-05-24 11:02:29 cri

Babbar jami'ar MDD mai lura da harkokin jin kai karkashin ofishin babban magatakardar majalissar Valerie Amos, ta ce, akwai bukatar baiwa al'ummun da suka kauracewa gidajensu a kasar Sudan karin tallafi mai dorewa, musamman ma, a cewarta, mutanen da suke zaune yanzu haka a sansanonin 'yan gudun hijira har tsahon kimanin shekaru 10.

mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey ne ya rawaito wannan batu, yayin taron ganawa da 'yan jaridu na rana rana da yake gabatarwa a birnin Khartoum. Wannan tsokaci nasa ya biyo bayan kammala ziyarar aiki da Amos din ta yi a kasar ta Sudan ranar Alhamis 23 ga watan nan.

Mai magana da yawun MDD ya ce, ziyarar Amos na da manyan manufofi guda biyu, wato duba halin da ayyukan jin kai ke ciki a kasar, tare kuma da karfafa gwiwa, da aminci tsakanin MDD da sassan masu ruwa da tsaki, ta yadda majalissar za ta samu isasshiyar damar cimma burin da aka sanya a gaba, a fannin ba da agajin jin kai a kasar ta Sudan.

Del Buey ya rawaito Amos na cewa, akwai tarin kalubale a gaban MDD, musamman idan aka yi duba da yawan al'ummar dake zaune a matsugunan 'yan gudun hijira sama da miliyan 1 da dubu dari hudu, da kuma mazauna yankin Dafur, da mafi yawansu ke fama da matsalolin rashin isassshen ilimi, da kayayyakin kiwon lafiya.

Don haka a cewarta, wajibi ne a kafa wani managarcin tsari, da zai ba da damar samar da ci gaba, da share fagen gudanar da ayyukan jin kai yadda ya kamata, a hannu guda kuma Amos ta ce, babban burin MDD ne ta ga an dakatar da fadace-fadace a dukkanin yankunan kasar ta Sudan, tare da warware matsalolin kasar ta hanyar lumana.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China