in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana damuwa dangane da tabarbarewar al'amura a gabashin Sudan ta Kudu
2013-05-15 10:12:15 cri

A ranar Talata 14 ga wata ne MDD ta bayyana damuwa matuka game da tabarbarewar al'amura a wasu sassan gabashin Sudan ta Kudu, inda ta yi kira ga gwamnati da ta hanzarta daukar matakai kan wannan al'amari.

Kakakin MDD Martin Nesirky, ya fada yayin taron manema labarai a ranar Talata cewa, tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke aiki a Sudan ta Kudu (UNMISS) ta bayyana a ranar Talata cewa, ta damu matuka game da lalacewar al'amura a ciki da wajen garin Pibor da ke jihar Jonglei.

Nesirky ya ce, tawagar ta yi Allah-wadai da yadda ake samun tashin hankali, kwasar ganima, da kuma yadda rikicin ke shafar fararen hula da hukumomin jin kai dake aiki a wurin.

Bugu da kari, kakakin na MDD, ya ruwaito tawagar ta UNMISS tana cewa, hakkin gwamnatin Sudan ta Kudu ne ta kare rayukan al'ummar da ke wurin, sannan ta yi kira ga fararen hula da hukumomin soja, da su hanzarta shawo kan al'amarin tare da hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.

Ya bayyana cewa, dakarun tawagar sun gudanar da sintiri a garin na Pibor tun kafin a fara kwasar ganiman, inda tawagar ta kara tura dakaru zuwa garin tun kafin wannan al'amari ya faru. An kuma baiwa dakarunta da ke aikin wanzar da zaman lafiya umarni da su taimaka wajen kare fararen hula.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China