in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin magatakardar MDD ya bukaci goyon bayan kasashen duniya domin sake gina Somaliya
2013-05-10 10:04:38 cri

Mataimakin babban sakataren MDD Jan Eliasson a jiya Alhamis 9 ga wata ya jaddada muhimmancin dake akwai na ba da goyon baya na gamayya daga kasashen duniya ga kasar Somaliya a kokarin da take yi na sake gina kanta.

Mr. Eliasson, da yake bayanin ma manema labarai game da sakamakon ziyarar shi ta kwanan a kan babban taron da aka kira a kan kasar Somaliya a birnin Landan, ya ce, babban kalubalen dake gaban shugaban kasar na Somaliya Hassan Sheikh Mohamud shi ne ya tabbatar da ikonsa a daukacin kasar, sannan ya karfafa zumunci da kasashe dake makwabtaka da kasarsa.

Shi dai taron da shugaban kasar Somaliya da firaministan Birtaniya David Cameron suka yi shi cikin hadin gwiwwa, an kira shi ne a wani lokaci da Somaliyan ke da bukatar a taimaka mata, ganin yadda ta fuskanci wargajewa sakamakon yaki tun daga 1991, kuma yanzu ne ta samu daidaito.

A shekara ta 2011, masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama sun janye daga Mogadishu, babban birnin kasar, abin da ya kawo kafuwar sabuwar gwamnati bayan da aka kammala wa'adin gwamnatin rikon kwarya. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China