A jiya Laraba 22 ga wata, 'yan majalissar dokokin kasar Somaliya suka janye yunkurinsu na jefa kuri'ar raba gardama a kan ayyukan gwamnatin firaminista Abdi Farah Shirdon mako guda da aka gabatar da shi a gabansu.
Shi dai wannan kuduri, 'yan majalissar kusan su 100 ne suka gabatar da shi suna zargin gwamnatin da rashin tabuka komai.
Kakakin majalissar Mohammed Osman Jawari ya bayyana a lokacin zamansu a jiyan cewa, yawancin wadanda suka dauki nauyin gabatar da wannan kuduri sun yanke shawarar yin watsi da shi, yana mai bayanin cewa, daga cikin 'yayan majalissar 93 da suka dauki nauyin gabatar da wannan kuduri sun janye suka bar guda 38 kawai, don haka ba za'a iya ci gaba da sauraran wannan kuduri ba, balle har a jefa kuri'a a kansa.
Daya daga cikin 'yan majalissar da suka dauki nauyin gabatar da wannan kuduri a baya, Abdullahi Haji ya sanar da majalissar a zaman da suka yi a Mogadishu, babban birnin kasar cewa, shi da sauran abokan aikin shi sun janye wannan kuduri ne tare da la'akari da yanayin kasa da al'ummarta kuma hakan ya biyo bayan wata yarjejeniya da suka cimma.
A baya dai, an tsige manyan jami'an gwamnati da dama sakamakon jefa kuri'ar kin amincewa da ayyukansu da majalissar ta yi.
Shi dai wannan firaministan dake ci yanzu Abdi Shirdon da aka nada shi fiye da watanni 7 da suka gabata ya hada gwamnati mai ministoci 10 wadanda suka samu amincewa mai karfi daga 'yan majalissar a watan Nuwamban bara.
'Yan majalissar dokoki na da karfin kafa doka in dai har suka samu babban rinjaye da ake bukata na kashi daya daga cikin biyar na 'yan majaliassa guda 275.(Fatimah)