in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Somaliya suna da 'dan shakku game da sakamakon taron Ingila
2013-05-07 12:18:04 cri

Ganin tawagar karshe ta tashi zuwa Ingila a ranar Asabar din da ta gabata domin halartar taron kasa da kasa da aka bude a London, babban birnin kasar Birtaniya, mazauna Mogadishu, fadar gwamnatin kasar sun bayyana 'dan shakkunsu game da sakamakon da za'a samu dangane da tattaunawar da za'a yi.

Shugaban kasar Somaliyan Hassan Sheikh Mohammed ya jagoranci tawagar kasar da ta kunshi ministocin gwamnati da 'yan majalissar wakilai da manyan jami'an gwamnati, inda zai shugabanci wani fannin taron tare da firaministan Birtaniya David Cameroun.

Wannan taron na Landan, in ji bayanin da ministan harkokin wajen Somaliya Fawzia Haji Yusuf ya yi, ya ce, zai mai da hankali ne a kan bukatun gwamnatin kasar Somaliya da kuma ba da taimakon da zai iya inganta bangaren tsaro, yin kwaskwarima a bangaren shari'a, sake daidaita da kuma samar da kafar zuba jari a tattalin arzikin kasar.

Da dama sun nuna fatan wannan taro na Ingila zai bude hanyar da za'a samu daidaito ta bangaren siyasar kasar tsakanin ita kanta gwamnatin kasar da yankin arewa maso yammacin kasar da ta ikirarin samun cikakken 'yancin kanta daga sauran bangaren kasar a 1991.

Tattaunawar ta Ingila za ta samu halartar kasashe 50 tare da kungiyoyin kasa da kasa, kuma wannan shi ne karo na biyu da aka shirya irin shi domin kasar ta Somaliya. An gudanar da na farkon a shekara ta 2012 wanda ya biyo bayan kawo karshen gwamnatin rikon kwarya da aka yi na tsawon shekaru 12 da kuma kafuwar sabuwar cikakkiyar gwamnati a kasar.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China