An shirya wani taron kasa da kasa a kan kasar Somaliya a birnin London ranar Talata, inda kasashe da kungiyoyin kasa da kasa suka amincewa samar da tallafi ga gwamnatin kasar Somaliya a fuskar tsaro, shari'a da kuma tafi da kudaden gwamnati.
Taron da aka yi akan kasar Somaliya, wanda Burtaniya da Somaliya suka karbi bakuncinsa, an gabatar ne a harabar Lancaster dake birnin London, kuma wakilai daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 54 ne suka halarta.
A jawabin karshen taron, mahalartan sun amince ma daukar kwararran matakai wajen tallafawa gwamnatin kasar Somaliya a muhimman sassa guda uku, wato a fuskar tsaro, shari'a da kuma tafi da kudaden gwamnati.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, samun ci gaba a fuskar siyasa shi ne abu mafi muhimmanci don tabbatar da dorewa na dogon lokaci a kasar Somaliya, kana al'ummar duniya ta yi maraba da kudurin gwamnatin kasar na gudanar da zabe a shekarar 2016.
Sanarwa har wa yau ta kara da cewa, mahalarta taron sun nuna dagewarsu na yin aiki da kasar Somaliya wajen kawar da 'yan fashin teku, da sauran laifuffuka da ake aikatawa a kan tekun, kana suna nuna goyon baya ga kokari da gwamnatin Somaliya take yi a yanzu na kafa yankin ikonta a teku.
Ita kuma a nata bangare, gwamnatin kasar Somaliya na kira ga abokanta na kasa da kasa da su samar da kudade ga shirin tsare-tsare na kasar Somaliya.(Lami)