Xi ya bayyana cewa, kasar Trinidad and Tobago kasar farko ce da ya kai ziyara a yankin Caribbean bayan da ya hau kujerar shugaban kasar Sin, kana ita ce zango na farko a ziyararsa a yankin Latin Amurka da Caribbean. Yayin wannan ziyara, ana sa ran kara hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, da kuma inganta dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi.
Shugaba Carmona ya bayyana cewa, kasarsa tana son kara yin mu'amala tare da kasar Sin da yin hadin gwiwa a tsakaninsu musamman a fannonin tattalin arziki, cinikayya, makamashi masu tsabta, kiyaye muhalli da dai sauransu. Kana kasarsa na fatan kara yin mu'amalar al'adu a tsakaninta da kasar Sin, da kuma kara fahimtar juna da zurfafa zumunci.