in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da shugaban Tanzania-Zanzibar
2013-05-28 20:13:39 cri

A ran 28 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa Ali Mohamed Shein na kasar Tanzania-Zanzibar wanda ya zo ziyarar aiki a nan Beijing.

Xi Jinping ya ce, a yayin da kai ziyara a kasashen Afirka a watan Maris da ta gabata, ya fahimci cewa, nahiyar Afirka nahiya ce dake cike da kuzari da neman na kansu, don haka kasashen Afirka za su iya samun ci gaba kamar yadda ake fata.

Kana ya ce, jama'ar kasashen Sin da Afirka suna kaunar juna tsakaninsu da Allah, a don haka kara bunkasa hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka buri ne da ake son cimmawa. Shi ya sa kasar Sin take son kara yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, ta yadda za su iya samun ci gaba tare, har ma za a iya karfafa sabuwar huldar abokantakar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare a wani sabon matsayi sannu a hankali.

A bangaren nasa kuma, shugaba Ali Mohamed Shein na Zanzibar ya bayyana cewa, ziyarar da shugaba Xi ya yi a kasar Tanzania ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa huldar dake tsakanin kasashen biyu. Ya yi bayanin cewa, kasar Zanzibar ta nuna godiya ga tallafi da taimakon da kasar Sin ta dade tana samar mata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China