Qin Gang ya bayyana cewa, ziyarar shugaban Xi a nahiyar Amurka na da cikakkiyar ma'anar musamman. A yayin shawarwarin da za a yi tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka, bangarorin biyu, za su yi musayar ra'ayi game da batutuwan duniya, da na shiyya-shiyya da suka dora muhimmanci sosai a kai. An yi imani cewa, wannan ziyara za ta yi amfani wajen raya dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata, da sa kaimi ga samar da zaman lafiya, da wadata, da karko a kasashen duniya, da na shiyya-shiyya. A ranar 26 ga wata zuwa ranar 28 ga wata, mai ba da taimako ga shugaban kasar Amurka ta fuskar tsaro Thomas Donilon, zai kawo ziyara a nan kasar Sin daga ranar 26 zuwa ranar 28 ga wata, don share fage game da shawarwarin da za a yi tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka.
Qin Gang ya ci gaba da cewa, ziyarar shugaban Xi a kasashen TrinidadandTobago, Costa Rica, Mexico za ta karfafa dangantakar bangarorin baki daya, kuma za ta cusa sabbin abubuwa game da dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen dake nahiyar Amurka ta Kudu da yankin Caribbean.(Bako)