Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta yi gargadi a ranar Alhamis cewa, tattalin arzikin kasar yana fuskantar wani mumman yanayi kuma kamata ya yi a kara daura damara domin maido da tattalin arzikin bisa kan turbar da ta dace.
Shugaban kasar ta Afirka ta Kudu Jacob zuma ne ya bayyana hakan, sakamakon wani rahoton alkaluman watanni hudu na farkon shekara na ci gaban GDP din kasar da aka fitar ranar Talata, wanda ya kai kashi 0.9 cikin 100 da aka fitar da kuma rashin daidaiton bangaren hakar ma'adinai sakamakon yajin aikin ma'aikatan hakar ma'adinan kasar na baya-bayan nan.
Alkaluman sun nuna cewa, bangaren hakar ma'adinar a kasar ta Afirka ta Kudu, yana daya daga cikin kafafofin da kasar ke samun ci gaban tattalin arzikinta.
A ranar Alhamis ne kudin kasar ta Afirka ta Kudu wato rand ya yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin shekaru 4 kan dalar Amurka, inda ake musayar da rand 10 kan dalar Amurka 1, inda ya zama kudi maras daraja tun tsakiyar watan Maris din shekara ta 2009.
Shugaba Zuma ya ce, muddin ana bukatar a cimma mizanin ci gaban da ake bukata, kamata ya yi gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta zage damtse wajen yayata bukatar ci gaban tattalin arzikin kasar.(Ibrahim)