in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu na maraba da rawa da Belarus za ta taka a fuskar ayyukan ababan more rayuwa
2013-05-14 10:32:23 cri

Kasar Afirka ta Kudu na maraba da shigowar kasar Belarus a fuskar manyan ayyukan ababan more rayuwa a Afirka, in ji wani babban jami'in gwamnati yayin ziyara ranar Litinin.

Mataimakin ministan dangantakar kasa da kasa da hadin gwiwa na kasar Afirka ta Kudu Marius Fransman shi ne ya bayyana hakan bayan ya halarci zaman shawarwari tsakanin ministocin Belarus da Afirka ta Kudu.

Fransman ya ci gaba da cewa, Belarus za ta yi gagarumar gudummawa wajen aiwatar da manyan ayyukan ababan more rayuwa a Afirka a kuma fannoni daban daban, har ma da fasaha da albarkatun jama'a.

Ya kuma jadadda muhimmancin shawarwari tsakanin kasashen biyu, inda ya ce, kasashen Belarus da Afirka ta Kudu kasashen 'yan ba ruwanmu ne, don haka ya dace su kafa hadin gwiwa ta hanyar wannan kafa.

Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Belarus Elena Kupchina ta bayyana cewa, Belarus da Afirka ta Kudu suna da matsaya iri daya kan batutuwa na duniya, don haka ya kamata a kara inganta hadin gwiwa a fuskar cinikayya da kawancen tattalin arziki.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China