in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dandalin tattalin arzikin duniya ya samar da kyakkyawan hanyar fito da Afrika
2013-05-09 10:26:37 cri

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya ce, dandalin tattalin arziki na duniya da aka bude a ranar Laraba 8 ga wata a birnin Cape Town ya samar da kayakyawan hanyar fito da nahiyar Afrika.

Dandalin wanda kasar Afrika ta Kudu ta dauki nauyin shiryawa yana gudanarwa ne daga ran 8 zuwa 10 ga wata a karkashin jigon "Isar da alkawarin Afrika". A matsayin na 23 da aka shirya da zummar samar da wata kafa mai muhimmanci ga shugabannin yankuna da na duniya baki daya.

Shugaba Zuma ya ce, wannan dandalin ya zo ne a daidai lokacin da nahiyar Afrika take bikin shekaru 50 da kafuwar kungiyar tarayyar kasashen Afrika da aka san ta da OAU.

Shugabannin kasashen, masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki da shugabannin masana'antu na duniya kuma za su tattauna a kan al'amura da suka shafi tattalin arzikin duniya da mai da hankali musamman a kan Afrika.

A yanzu haka, shugabannin kasashe da gwamnatoci 9 da suka hallara sun hada da Goodluck Jonathan na Nigeriya wanda yake ziyarar aiki a kasar ta Afrika ta Kudu.

Shugaba Zuma ya yi bayanin cewa, Afrika ta Kudu za ta yi amfani da wannan dandali domin tallata shirye-shiryenta na ayyukan cigaban kasa domin jawo hankalin masu zuba jari a fannoni 6 na manyan ayyukan kasar da suka hada da aikin noma, hakar ma'adinai, sarrafa kayayyaki, yawon shakatawa, samar da ababen more rayuwa da kuma samar da yanayi mai kyau na koren albarkatu.

Shi dai wannan dandali mai zama kansa dake da ofis a Geneva na kasar Switzerland ya dukufa ne wajen samar ma kasashen duniya kafar kasuwanci, siyasa, ilimin malaman makarantu da sauran shugabanni a cikin al'umma domin daidaita tsarin da kasashen duniya, yankuna da masana'antu ke bi.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China