Gwamnatin Afrika ta Kudu ta nuna yabo a ranar Talata kan kokarin da kasashen Amurka da Rasha suke yi domin shirya taron kasa da kasa kan rikicin kasar Syria.
Taro zai samu halartar gwamnatin Syria da masu adawa, ta yadda za'a ganin an kawo karshen rikicin soja a wannan kasa, in ji Ebrahim Ebrahim, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Afrika ta Kudu.
Afrika ta Kudu ta yarda cewa, abu mafi kyau shi ne ba da goyon baya ga mafitar siyasa bisa kokarin gamayyar kasa da kasa cikin hadin kai wajen kai ga kafa gwamnatin wucin gadin bisa adalci da 'yan kasar Syria za su jagoranta da kansu domin tabbatar da wata kasar demokuradiyya, inda kananan kabilu za su samun kariya, in ji mista Ebrahim.
Haka kuma ya kara da cewa, gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta dauki niyyar ba da kwarin gwiwa ga dukkan bangarorin da wannan rikici ya shafa a kasar Syria domin cimma wani tsarin sasanta 'yan kasa na musammun wanda za'a kawo karshen tashe-tashen hankali, da matsin lamba ko sanya bakin wasu kasashen waje cikin harkokin kasar Syria bisa burin canja mulki. Ta wannan hanya ce kadai za'a iyar tabbatar da fatan samun 'yancin demokuradiyya ga mutanen kasar Syria, in ji mista Ebrahim. (Maman Ada)