Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana ranar Alhamis cewa, dangantaka tsakanin kasashen Rasha da Afirka ta Kudu na kara bunkasa kuma akwai alamun kyakkyawar makoma.
Yayin wata ganawa da shugaban kasar Afirka ta Kudu a yankin tekun Sochi, shugaban Putin ya bayyana cewa, yawan tuntubar juna tsakanin kasashen biyu ya nuna aminci dake tsakaninsu, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na da kyakkyawar makoma.
Shugaban na Rasha ya ci gaba da cewa, ya gamsu da dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu saboda harkar cinikayya tsakaninsu ya samu bunkasa da sama da kashi 66 cikin dari a 2012, sannan a watanni ukun farko na bana, ya karu da kashi 17 cikin dari.
A halin da ake ciki, kamfanonin Rasha da dama sun shiga kasuwannin Afirka ta Kudu, kana kamfanonin Afirka ta Kudu su ma sun fara gudanar da harkoki a kasar Rasha, in ji Putin.
A nasa bangare, shugaban Afirka ta Kudu Zuma ya yaba dangantaka tsakanin kasashen biyu, ya kuma amince cewa, Afirka ta Kudu da Rasha suna da abubuwa da dama da suka zo daya.
Ya ci gaba da cewa, a matsayinta na mamba a kungiyar BRICS wacce ta kunshi kasashe masu tasowa a fuskar tattalin arziki, wato Brazil, Rasha, Indiya da Sin, kasar Afirka ta Kudu tana da burin ganin sauran sassan duniya sun saurari nahiyar Afirka.(Lami)