in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan Afirka ta Kudu ya ce, yajin aikin ma'aikatan hakar ma'adanai ba shi da tasiri kan harkokin zuba jari
2013-05-16 10:31:17 cri

A ranar Laraba 15 ga watan nan ne ministan ma'aikatar ciniki da masana'antu a Afirka ta Kudu Rob Davies, ya bayyana cewa, yajin aikin da ma'aikatan hakar ma'adanai na Lonmin dake Marikana ke yi, ba zai gurgunta harkokin zuba jarin kasashen waje ba.

Wannan dai tsokaci da ya yi gaban zauren majalissar kasar, yayin da yake gabatar da kasafin kudin ma'aikatar tasa, na zuwa ne a gabar da duban ma'aikatan hakar ma'adanai suka kauracewa wuraren aikinsu a Marikana, a lardin arewaci, dake yankin arewa maso yammacin kasar.

Davies ya ce, masu zuba jari daga ketare ba za su razana ba, kuma za su ci gaba da kasancewa a kasar, ganin cewa, nahiyar Afirka ita ce makomar masu zuba jari a nan gaba, kuma kasar Afirka ta Kudu ce ta daya, a dukkanin fadin nahiyar, dake da karfin masana'antu.

Ministan ma'aikatar ciniki da masana'antu a Afirka ta Kudun ya kara da cewa, yawan kudaden zuba jarin waje da kasar ta samu a baya-bayan nan, ya kai dalar Amurka miliyan dubu 5 da dari 8.

Sai dai kafin wannan tsokaci nasa, ministar kwadagon kasar Mildred Oliphant, ta bayyana damuwarta da halin yajin aiki dake wanzuwa a Marikana, tana mai kira ga jagororin kungiyoyin kwadago 2, dake jagorantar wannan zanga-zanga, da su sanya manufar ci gaban kasa a gaban komai. Oliphant ta zargi kungiyoyin da daukar matakin fito-na-fito a wannan lokaci, matakin da a ganinta na iya haifar da da-maras-ido. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China