A ranar Talata, ofishin gudanar da harkokin bil adama ta MDD (OCHA), ta bayyana cewa, akwai bukatu matuka a bangaren jama'a a Gao dake gabashin kasar Mali inda ruwa da ake da shi na sha ga jama'a ya sauka zuwa kashi 60 cikin dari a makonni da suka gabata.
Mataimakin mai magana da yawun MDD Eduardo del Buey, yayin bayani da aka saba yi kullum, ya ce, wasu unguwanni a Gao ba su da ko digon ruwa saboda famfuna marasa aiki da rashin wutar lantarki, kana a wajen garin, kogin Niger ne kadai waje da ake dibo ruwa kuma akwai damuwa saboda fargabar barkewar cutar amai da gudawa ta kwalera. A yanzu dai cibiyoyin ba da agaji suna aikin daukar matakan rigakafi da ba da magunguna.
Cibiyar harkokin bil adama ta MDD ta tura ma'aikata biyu zuwa Gao kuma tana shirin bude ofishinta. Baki daya dai, akwai kungiyoyin ba da agaji sama da 100 a Mali.
Izuwa jiya Talata, asusun tallafawa kasar Mali ya taro kudi da suka kai kashi 29 cikin dari na yawan adadi da ake nema, wato dalar Amurka miliyan 410.
Marixie Mercado dake aiki da asusun kula da harkokin yara na MDD, UNICEF, na baiyanawa manema labarai cewa, har yanzu akwai matsala babba na rashin abinci masu gina jiki a fadin kasar, musamman a kudanci inda a can ne kashi 90 cikin dari na mutanen ke da zama.(Lami)