in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi kira da a dauki karin matakan murkushe kungiyar LRA
2013-05-30 10:05:58 cri

Wata sanarwa da kwamitin tsaron MDD ya fitar a ranar Laraba 29 ga watan nan, ta bukaci kasashen dake yankin tsakiyar nahiyar Afirka, da su dauki karin matakan murkushe barazanar da kungiyar 'yan tawayen nan ta LRA ke yiwa zaman lafiyar yankin.

Hakan ya biyo bayan zargin da MDD ta yi wa wannan kungiya, na kisan mutane da yawansu ya haura 100,000 a shekaru 25 da aka shafe ana tashe-tashen hankula a wannan yanki. Kwamitin tsaron MDD ya bukaci kasashen dake yankin da 'ya'yan kungiyar ta LRA ke tunga, da su baiwa batun kare hakkokin bil'adama kulawa ta musamman. Bisa wannan kuduri ne ma majalissar ta yabawa kokarin da kasashen Afirka ta Tsakiya CAR, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo DRC, da Sudan ta Kudu, da kuma Uganda ke yi don gane da hakan, tare da kira ga sauran kasashen dake yankin, da su hada karfi da karfe domin cimma burin da aka sanya gaba.

Sai dai duk da yunkurin da wadannan kasashe ke yi, sanarwar ta nuna damuwa kan koma baya da aka samu a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, don gane da yakin da ake yi da ayyukan kungiyar ta LRA, biyowa bayan juyin mulkin kasar na ranar 24 ga watan Maris da ya gabata, lamarin da sanarwar ta ce, ya sabbaba dagulewar yanayin zamantakewar al'umma, da kuma tsaron kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China