Hukumar ta ce wannan shi ne bankin shiyya na farko a yankin, kuma bankin kasuwanci mai ba da rance na farko da zai fara aiki a yankin mai cin gashin kansa tun lokacin da aka kafa ta.
Hukumar ta kara da cewa, Bankin sadarwa wanda ya kasance na biyar mafi girma a Sin zai kasance babban mai sanya jari na bankin. A cewar hukumar, kafa bankin a yankin na Tibet zai bunkasa harkokin kasuwanci kuma zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin shiyyar.
Bugu da kari, bankin zai taimakawa ci gaba kanana da matsakaitan masana'antu ta hanyar ba su taimakon kudi da kuma ayyukan da zasu inganta rayuwar mazauna wurin. (Ibrahim)