A cikin 'yan shekarun nan, sakamakon bunkasuwar tattalin arzikin jihar Tibet cikin sauri, yawan harajin da aka samu a jihar Tibet ya karu sosai. Daga shekara ta 2006, saurin karuwar yawan harajin da sassan buga haraji na jihar suka karba ya kai kashi 37.4 bisa dari. Haka kuma a cikin shekaru shida da suka gabata, jimillar yawan kudin harajin da aka karba ta zarce Yuan biliyan 35.8, abun da ya samar da taimako sosai ga ci gaban tattalin arziki da zaman lafiya da kwanciyar hankali na jihar. Ya zuwa shekara ta 2011, akwai gundumomi hudu a jihar Tibet wadanda yawan kudin harajin da suka samu ya zarce Yuan miliyan dari, kana akwai sama da kashi 70 bisa dari na gundumomin jihar wadanda suka samu kudin haraji fiye da Yuan miliyan 5.(Murtala)