in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arziki na jihar Tibet ta Sin yana ta karuwa da sauri cikin shekaru 20 da suka gabata
2013-01-04 10:57:06 cri

Jiya Alhamis 3 ga wata, gwamnan jihar Tibet ta kasar Sin mai cin gashin kanta Padma Choling ya bayyana a birnin Lhasa cewa, kiyasi na yawan kudin da aka samu wajen samar da kayayyaki, wato GDP na jihar ya kai kimanin kudin Sin Yuan biliyan 70.1 a bara. Wannan adadi ya nuna cewa jihar Tibet ta samu karuwar tattalin arziki fiye da kashi 10 cikin 100 cikin shekaru 20 a jere. Jimillar kudin da jihar ta samu wajen shige da ficen kayayyaki ta karu da kashi 170 cikin 100, kana yawan kudin shiga na manoma ya karu da fiye da kashi 15 cikin 100, sannan yawan kudin shiga na mazauna birane da kauyuka ya karu da kashi 11 cikin 100.

A shekara ta 2010, yawan GDP da jihar Tibet ta kasar Sin ta samu ya zarce Yuan biliyan 50, yayin da a shekarar 2011, wannan adadi ya haura zuwa Yuan biliyan 60.5. A kuma shekarar 2012, an kiyasta cewa, wannan adadi zai haura zuwa Yuan biliyan 70.1, wato ke nan, jihar ta cimma burin samun karuwar GDP da yawansa ya zarce Yuan biliyan 10 har cikin shekaru 3 a jere.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China