Bisa labarin da hukumar kula da yawon shakatawa ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta Sin ta bayar, an ce, a shekarar 2012, jihar Tibet ta jawo masu yawon shakatawa da yawansu ya kai miliyan 10.584, wanda ya nuna karuwa da kashi 21.7 cikin 100, yayin da yawan kudin shiga da harkar yawon shakatawar ta samar ya kai Yuan biliyan 12.647, kuma abin da ya karu da kashi 30.3 cikin 100, wato ke nan harkokin yawon shakatawa ya samu habaka sosai.
Bisa labarin da wani jami'in hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet ya bayar, an ce, a shekarar 2012, jihar Tibet ta kara jawo hankalin masu yawon shakatawa sosai, ta kuma zama wurin da ake sa niyyar ziyara sosai.
Kazalika, an ce, kashi 98.2 cikin 100 na masu yawon shakatawa sun gamsu da yanayin yawon shakatawa a wurin, kuma kashi 73 cikin 100 na masu yawon shakatawa na da niyyar sake ziyartar jihar Tibet.(Bako)