Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya amince a ranar Laraba da kafuwar wani kwamitin dake kunshe da mambobi 26 domin tsagaita bude wuta tare da kungiyar Boko Haram, da har yanzu kungiyar ba ta ba da wata amsa mai gamsarwa ba game da wannan tayi.
Kwamitin zai hada da kusoshin kungiyar a cikin tattaunawa mai alfanu da za ta samar da wani yanayi mai kyau da zai taimaka ga warware wannan rikici na rashin tsaro a arewacin wannan kasa dake yammancin Afrika.
Kakakin shugaban Najeriya, Reuben Abati, ya tattabar da wannan labari a cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofi.
Kwamitin zai kuma fadada wani shiri domin ba da afuwa ga dukkan mambobin kungiyar Boko Haram tare da karbe makamai a cikin tsawon kwanaki 60, in ji mista Abati.
A karkashin jagorancin ministan harkoki na musammun, Kabiru Tanimu Turaki, kwamitin ya hada da shugabannin addinin Islama na arewacin kasar, mambobin majalisar dokoki, manyan jami'an soja, malaman jami'a, alkalai, shugabannin kungiyoyin kare hakkin dan Adam da kuma jami'an diplomasiyya. (Maman Ada)