Kasar Zimbabwe ta janye bukatar da ta gabatar ga MDD na neman tallafin kudaden gudanar da zabe bayan da aka gagara cimma makasudin bukatun da MDD, dangane da tawagar tantancewa da za ta kawo ziyara kasar.
Yayin taron manema labarai na hadin gwiwa a ranar Talata, ministan shari'a da harkokin doka Patrick Chinamasa ya ce, kasar Zimbabwe ba za ta nemi tallafi daga MDD ba saboda majalisar ta dage kan wasu ka'idoji wadanda kasar ke ganin cewa sun shafi ikonta.
A cikin wata sanarwa, ofishin MDD dake Harare ya bayyana cewa, an kintsa turo tawagar tantance bukatar (NAM) zuwa kasar Zimbabwe bayan da gwamnatin kasar ta nemi a taimaka mata a fuskar taro kudaden gudanar da zaben raba gardama kan dokoki da kuma babban zabe a kasar.
To amma a yayin da ake kan kokarin turo tawagar zuwa Zimbabwe, sai aka gano cewa, akwai wasu 'yan matsaloli da suka taso sakamakon sabanin tsarin tawagar tantancewar, in ji sanarwar.
Ana sa rai cewa, kasar Zimbabwe za ta gudanar da babban zabe a wannan shekara.
Gwamnatin kasar wacce a yanzu ke fama da matsalar rashin kudi ta nemi taimako daga MDD da kuma kasashen Afirka ta Kudu da Angola, bayan da ta gano cewa, ba ta da isassun kudaden gudanar da zaben.(Lami)