in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya gana da mataimakin firimiyan Sin Wang Yang
2013-05-23 10:15:39 cri

Mataimakin firimiyan kasar Sin Wang Yang, ya bayyana ziyarar da shugaba Xi Jingping ya kai wa nahiyar Afirka cikin watan Maris da ya gabata, a matsayin wata shaida dake nuna kyakkyawar alakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen nahiyar ta Afirka. Wang Yang ya yi wannan tsokaci ne lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, yayin ziyarar da ya fara a kasar ta Zimbabwe tun daga ranar Tatalar da ta gabata.

Har ila yau, Wang Yang, ya jaddada muhimmancin da kasar Sin ke baiwa dangantakar kawance dake tsakaninta da Zimbabwe, yana mai cewa, alaka tsakanin bangarorin biyu na da dadadden tarihi.

Mataimakin firimiyan kasar ta Sin ya kuma jaddada aniyar Sin don gane da tallafawa kasashen Afirka a dukkanin fannonin ci gaba, tare da bayyana bukatar bude sabon shafin habaka dangantakar huldodin ci gaba tsakaninta da Zimbabwe, da ma nahiyar ta Afirka baki daya.

Da yake mai da jawabi, shugaba Mugabe ya nuna gamsuwa da kalaman Wang Yang, ya kuma yi fatan dangantakar dake tsakanin kasarsa da Sin, za ta sake daukaka zuwa wani sabon matsayi.

Wata sanarwa da ta fito daga tawagar mataimakin firimiyan na kasar Sin, ta ce, yayin wannan ziyara, Wang Yang, ya gana da mataimakin shugaban kasar Joyce Mujuru, da firaminista Morgan Tsvangirai, ya kuma rattaba hannu kan wasu muhimman takardun yarjejeniyoyin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu.

A jawabin da ya yi yayin ganawarsa da Wang Yang, firaminista Morgan Tsvangirai, ya bayyana gamsuwarsa da irin tallafi da Sin ke baiwa Zimbabwe, yana mai cewa, kasarsa ta amfana daga fasahohin ci gaba irin na Sin, musamman a fannin ci gaban tattalin arziki. Daga nan sai ya yi kira ga 'yan kasuwar kasar Sin, da su shigo domin zuba jari a kasar ta Zimbabwe.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China