in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe ta yi fatali da bukatar shigar tawagar 'yan sa ido kasar yayin babban zaben ta dake tafe
2013-04-07 16:07:44 cri
Mahukuntan kasar Zimbabwe sun yi watsi da bukatar da aka gabatar musu ta bai wa tawagar masu sanya ido ta gida da ta waje damar lura da yadda babban zaben kasar zai wakana, duk kuwa da alkawuran da ke tattare da wannan bukata.

Rahotanni dai sun bayyana yadda mataimakin sakataren harkokin wajen kasar Amurka mai lura da harkokin da suka shafi nahiyar Afirka Johnie Carson ya aika wa ofishin mataimakin shugaban kasa da kuma ministan harkokin wajen kasar ta Zimbabwe wasiku, wadanda ke kunshe da bayanai masu nuna gamsuwarsa da ikon mahukuntan kasar na gudanar da sahihin zabe, tare da bukatar tsagin mahukuntan su amince da bukatar sanya ido ga gudanar da zaben dake tafe. Wadancan wasiku sun kuma kunshi alkawarin nemawa kasar kudaden tallafi, da kuma duba yiwuwar dage takunkumin da aka kakabawa kasar, muddin dai ta amince da waccan bukata ta shigar 'yan sa ido.

A nata bangare gwamnatin kasar ta Zimbabwe, ta yi fatali da wannan tayi, kamar dai yadda shafin yanar gizon jaridar gwamnati ta Herald ya ruwaito kakakin fadar shugaban kasar George Charamba na cewa, ba za su amince da wannan kuduri da Carson ya gabatar musu ba, musamman duba da yadda ya amince da ikonsu na iya gudanar da zabe managarci, yayin da a daya hannun yake bukatar su ba da damar a tsoma bakin wasu, a harkar da ta shafi cikin kasarsu. Daga nan sai Charamba ya jaddada matsayin gwamnatin kasar, don gane da ba da damar tsoma bakin kasashen waje cikin harkokin mulki, yana mai cewa, ba sa bukatar wancan tallafin da aka alkawarta musu, musamman daga mutanen da ya kira dakin haure.

Ana dai sa ran kasar Zimbabwe za ta gudanar da babban zaben kasar ne ko dai a watan Yuni, ko kuma watan Satumaba na wannan shekarar da muke ciki, matakin da ake fatan zai kawo karshen gwamnatin hadakar kasar mai tattare da tarin matsaloli. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China