in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin firimiyan kasar Sin ya fara ziyarar aiki a Zimbabwe
2013-05-22 10:37:03 cri

A jiya Talata 21 ga wata, Mataimakin firimiyan kasar Sin Wang Yang ya isa birnin Harare, domin fara ziyarar aiki a kasar Zimbabwe wanda shi ne zangon shi na farko a ziyarar shi zuwa kasashen Afrika da zai yi tsakanin 21 zuwa 25 ga watan nan da muke ciki domin karfafa zumuncin dake tsakanin kasarsa da nahiyar Afrika.

A cikin wata sanarwa a hukumance da aka fitar da isarsa, Wang Yang ya ce, zumuncin dake tsakanin Sin da Zimbabwe sun gwada karfinsa kuma sun ga yana kan karfafa duk da yanayin da ake ciki na sauyin lokaci da dangantaka na kasashen waje.

Ya ce, don haka Sin ta dauki Zimbabwe a matsayin wata 'yar uwarta, aminiya kuma abokiyar hulda wanda shi ya sa take da zummar kara inganta mutuncin dake tsakaninsu a siyasance, ta kuma fadada hadin kai da zai amfana ma juna ya kuma karfafa abota da ita.

A lokacin wannan ziyararsa, Mr. Wang zai gana da shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, mataimakiyar shugaban kasar Joyce Mujuru, sannan kuma zai ziyarci firaministan kasar Morgan Tsangirai bayan ya rattaba hannu a kan wassu yarjejeniyoyi na hadin gwiwwa tsakanin kasashen biyu.

Kafin haka sai da mataimakin firaministan ya riga ya gana da 'yan kasuwa na kasar Sin dake zaune a Zimbabwen a ofishin jakadancin kasar Sin dake birnin Harare, fadar Gwamnatin kasar, inda suka mashi bayani game da yadda suke tafiyar da kasuwancin da suke yi a kasar wanda suka hada da hakan ma'adinai, samar da ababen ayyukan zamani na aikin gona da kuma sadarwa.

Mr. Wang ya ce, hadin gwiwwar tattalin arziki tsakanin kasar Zimbabwe da kasar Sin yana da matukar muhimmanci wanda yake kamar wani ginshiki ne na amincin dake tsakaninsu.

Mataimakin firaministan Sin ya kai wannan ziyara a daidai lokacin da tattalin arziki sakamakon huldar dake tsakanin kasashen biyu ke kara habaka, a shekarar bara ta 2012, huldar cinikayya tsakanin kasashen ya haura da ribar fiye da dalar Amurka biliyan daya, abin da ya sa kasar Sin ta zama kan gaba wajen zuba jari a Zimbabwe.

Bayan wannan ziyara, Wang Yang zai kuma halarci bikin cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU wadda ta fara amsa sunan OAU a matsayin wakilin shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda za'a yi a cibiyar kungiyar dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

Idan ba'a manta ba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci kasashe 3 a nahiyar Afrika wato Tanzaniya, Afrika ta Kudu da kuma Kongo a matsayin ziyararsa ta farko zuwa kasashen waje jim kadan da darewa kan wannan kujera.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China