in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cafke wani tsohon ministan Cote d'Ivoire a kasar Ghana
2013-01-18 15:51:54 cri

Tsohon ministan matasan kasar Cote d'Ivoire, Charles Blegude ya shiga hannun hukumomin tsaron kasar Ghana, a wani labarin da cibiyar tsaron kasar Ghana ta bayar a ranar Alhamis. Blegude ya shiga hannu bisa takadar sammacin dake kansa, ana kyautata zaton za'a tusa keyarsa zuwa kasar Cote d'Ivoire, a cewar wannnan majiya.

Sery Zadi, mamba na jam'iyyar FPI dake hijira a kasar Ghana da kamfanin dillancin labarai ya tuntuna ya tabbatar da wannan labari cewa, ana tsare da Blegude tun ranar Alhamis a gidansa dake Tema, mai tazarar kilomita 30 daga gabashin birnin Accra.

Ko da yake babu wata tuhuma da ake wa Blegude, sai dai ana zaton hukumomin na Ghana za su tabbatar masa da laifin dake bisa wuyansa a wannan rana, in ji mista Zadi.

Sery Zadi, kakakin 'yan gudun hijiran kasar Cote d'Ivoire a kasar Ghana ya bayyana cewa, akwai wasu tuhume tuhume da ake wa Blegude baya ga laifin cin zarafin bil Adama da kuma ake zargin sauran mutanen da tuni suke tsare. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China