Kasar Sin ta ba da taimakon kudi na Sefa miliyan 50 ga hukumar zabe mai zaman kanta (CEI) a ranar Alhamis domin shirya zaben kananan hukumomin ranar Lahadi mai zuwa a kasar Cote d'Ivoire. Taimakon na kasar Sin na da manufar baiwa hukumar CEI kwarin gwiwa wajen shirya kananan zabubuka yadda ya kamata, in ji jakadan kasar Sin dake Cote d'Ivoire, mista Zhang Guoqing.
Jami'in diplomasiyyar na kasar Sin ya nuna cewa, wannan taimako na bayyana jin dadin gwamnatin kasarsa kan yadda wannan hukuma ta CEI ta yi aiki tun lokacin zaben shugaban kasa na watan Nuwamban shekarar 2010.
A nasa bangare, shugaban hukumar CEI, Youssouf Bakayoko ya bayyana jin dadinsa da yardar da ake nuna wa hukumar da yake jagoranta, da nuna yabo kan taimakon kudi da na kayayyaki da kasar Sin take bayar wa ko da yaushe a duk lokacin zabe.
A ranar Lahadi ne za'a gadanar da zaben kananan hukumomi a dukkan fadin kasar Cote d'Ivoire ba tare da jam'iyyar (FPI) tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ba dalilin niyyar kauracewa zaben da ta dauka kamar yadda ta yi a lokacin zaben 'yan majalisa a shekarar 2011. (Maman Ada)