in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana cigaba da kada kuri'u na zaben kananan hukumomi a Cote d'Ivoire
2013-04-22 14:54:20 cri

Zaben kananan hukumomi a kasar Cote d'Ivoire, da jam'iyyar tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ta kaurace ma na gudanarwa cikin kwanciyar hankali ba tare da wani babban sauyi ba. A akasarin runfunan zabe da aka bude da 'dan jinkiri kadan, dalilin isowar kayayyakin zabe ko kuma na jami'an aikin zabe, zaben na gudanarwa sannu a hankali. Babu wani dogon layi, babu wata hayaniya ko kuma wani cunkuso a gaban runfunan zabe, inda masu kada kuri'u ba su nuna gaggawar zuwa cika aikinsu na 'yan kasa a cikin yawancin unguwannin dake birnin Abidjan. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China