Wata sanarwar da kamfanin sadarwa na kasar Senegal SONATEL ya fitar ta nuna cewa, a shekarar da ta gabata, kamfanin ya samu ribar da ta kai dalar Amurka miliyan 348. Adadin da ya kai kaso 11 bisa dari, kari kan abin da kamfanin ya samu a shekarar 2011.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, wannan nasara na da nasaba da karin huldodi da kamfanin ya aiwatar a kasashen Guinea da kuma Guinea Bissau.
Shi dai kamfanin na SONATEL wanda aka kafa ta hanyar hade kamfanin gidan waya da na sadarwar kasar ta Senegal a shekarar 1985, na gudanar da harkokin cinikayyarsa ne a kasashen dake yammacin Afirka tun cikin shekarar 2006. Shi ne kuma kamfanin sadarwa mafi girma a kasar.(Saminu)