Kasar Senegal ta dauki niyyar ajiye takarar neman kujerar zama mamba ba na dindindin ba a kwamitin sulhu na MDD na wa'adin shekarar 2014 zuwa shekarar 2015, a lokacin zabubukan da za'a gudanar a shekarar 2013, a yayin babban taron MDD karo na 68 a wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu daga wata majiya mai tushe a ranar Talata.
A cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar Senegal ta fitar, shugaban kasar Senegal Macky Sall ya sanarwar wannan takara, a yayin ziyarar aiki da sada zumunci da ya kai a birnin Conakry a ranakun Lahadi da Litinin da suka gabata a gaban takwaransa na kasar Guinee Alpha Conde wanda tuni ya ba da goyon bayansa.
Haka kuma ma'aikatar harkokin wajen Senegal, ta bayyana cewa, wannan ziyara na bisa tushen kara karfafa dangantaka, abokantaka da makwabtaka tsakanin kasashen biyu, tare kuma da baiwa shugabannin damar jaddada niyyarsu ta kara dankon zumunci tsakanin al'ummomin kasashen biyu. (Maman Ada)