in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Burtaniya ya yi kiran da a hanzarta kawo karshen rikicin Syria
2013-05-14 10:19:10 cri

A ranar Litinin ne firaministan Burtaniya David Cameron ya yi kira ga kasashen duniya da su kara himma don kawo karshen rikicin da ya dabaibaye kasar Syria

A wani taron manema labarai da ya gudanar da shugaban Amurka Barack Obama, bayan ganawarsu a fadar White House, Cameron ya ce, dukkansu sun goyi bayan yunkurin shugaban Rasha Vladimir Putin na kokarin ganin an kawo karshen rikicin da aka shafe watanni 27 ana tafbakawa a kasar da ke gabas ta tsakiya, ta yadda 'yan kasar ta Syria za su amince da kafa gwamnatin da za ta kunshi kowa da kowa.

Kasashen Amurka da Rasha sun amince su shirya wani taron zaman lafiya a Geneva a karshen watan Mayu, inda za a hallara wakilan gwamnati da na 'yan adawan Syria a kan teburin sulhu.

Cameron ya bayyana ganawarsa da Putin a makon da ya gabata a matsayin babbar nasara, inda ya ce, akwai bukatar kasashen duniya su hada kai cikin gaggawa don kawo karshen kashe-kashen da ake yi a Syria.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China