A ranar Laraba, magatakardar MDD Ban Ki-Moon ya yi maraba da matsaya da kasashen Rasha da Amurka suka cimma don gane da warware rikicin kasar Syria.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun magatakardar MDD na nuni da cewa, magatakardar ya yi maraba da sanarwar da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, da na kasar Amurka John Kerry suka bayar jiya a birnin Moscow.
Magakardar MDD da wakilin kungiyar tarayara kasashen Larabawa da kuma MDD kan rikicin Syria Lakhdar Brahimi sun dage tun da farko kan cewa, warware rikicin ta hanyar siyasa shi ne mafita ga rikicin da ya dade yake kuma kara zurfi, in ji sanarwar
Sanarwar ta ci gaba da cewa, kamata ya yi kowa ya fahimci abin da aka sa a gaba, wato a kawo karshen rikicin, a samu sauyi daga abubuwa na baya da kuma shiga sabon tsari a Syria wanda zai kiyaye 'yancin dukkan al'umomi da kuma cimma burin daukacin jama'ar Syria na samun 'yanci, adalci, da mutunci.
MDD ta kiyasta cewa, mutane miliyan 6.8 dake cikin kasar Syria na matukar bukatar agaji, inda kusan rabin wannan adadi yara kanana ne.(Lami)