in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Falasdinu ya ce, ba za su amince da kan iyakoki na wucin gadi ba
2013-05-27 10:05:57 cri

A ranar Lahadi ne shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya bayyana cewa, Falasdinawa ba za su amince da kasa mai kan iyakoki na wucin gadi ba.

Yayin jawabi a taron tattalin arziki na duniya da aka yi a kasar Jordan wanda ya samu halarcin shugaban kasar Isra'ila Shimon Perez da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, shugaba Abbas ya ce, kan iyakoki na wucin gadi ba za su kawo karshen rikicin ba, sai dai ma su kara tsawaita lokacin.

Shugaban na bukatar a kafa kasar Falasdinu ta amfani da kan iyakoki na 1967, inda ya yi kira ga Isra'ila da ta amince da matakan zaman lafiya da kasar Saudi Arabiya ta gabatar a shekarar 2002, wanda ya samu amincewar kasashen Larabawa baki daya.

Matakan zaman lafiyan sun yi wa kasar Isra'ila tayin dangantaka tsakaninta da kasashen Larabawa, sannan ita kuma ta janye daga yankunan da ta mamaye tun shekarar 1967.

Abbas ya ce, wannan shawara na da muhimmanci ga kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru ana fama da shi tsakanin bangarorin biyu don a samu zaman lafiya.

Kerry, a nasa bangare, ya yi kira ga Isra'ila da Falasdinu da su kulla yarjejeniya ta siyasa, inda ya yi gargadin cewa, rashin zaman lafiya na iya janyo yaki.

A halin da ake ciki, shugaba Perez ya nanata muhimmancin maido da zaman tattaunawa tsakanin Isra'ila da Falasdinu ba tare da bata lokaci ba domin a kawo karshen rikicin da kafa zaman lafiya.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China