Manyan jami'an soja da 'yan majalisar dokokin kasashen yammacin Afrika, na mai da hankali kan bullo nagartattun matakan yaki da ta'addanci a wannan shiyya ranar Alhamis da safe a Yamai, babban birnin kasar Nijar.
Wannan wata dama ce da za a baiwa mahalarta taron tattaunawa kan manyan batutuwan da suka shafi dalilan kalubaloli, illar kungiyoyin 'yan ta'adda a wannan shiyya, kuma za a gabatar da mafita a karshen wannan dandalin kasa da kasa, ta yadda za'a iyar kaucewa bazuwar ayyaukan ta'addanci a yammacin Afrika.
Ministan tsaron kasar Nijar, Karidjo Mahamadou ya sheda wa mahalarta taron cewa, muhimmanci da kwarewar muhawarorin za su bullo da hanyoyi masu alfanu ga kasashen wajen tanadar matakai da nagartattun kayayyakin yaki da ta'addanci, ta yadda za'a mai da hankali kan samun bunkasuwa da kyautatuwar zaman al'ummomin shiyyar.
Tun yau da kusan shekara daya, yammacin Afrika na fama da matsalar rashin tsaro a wurare daban daban, musammun ma a kasar Mali, arewacinta dake iyaka da kasar Nijar, tare da kungiyoyin ta'addancin dake alaka da kungiyar Al-Qaida a yankin Maghreb da kuma kasar Najeriya tare da matsalar kungiyar Boko Haram a arewacin kasar, in ji mista Karidjo. (Maman Ada)