in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta mayar da 15% na kudin da ake samu daga ma'adinai da man fetur ga yankunan da abun ya shafa
2013-05-17 10:18:30 cri

Gwamnatin kasar Nijar ta dauki niyya yanzu na mayar da kashi 15 cikin 100 na kudaden da take samu daga sayar da albarkatun ma'adinai da na man fetur ga wasu yankunan kasar da harkar wannan arziki ya shafa.

Gwamnatin kasar ta yi haka domin ba da hadin kai da matakin da 'yan majalisar dokokin kasar suka dauka na kawo gyara fuska kan wasu kudurorin da suka shafi kudin man fetur da kudurin ranar 2 ga watan Maris na shekarar 1993 da ya shafi dokar kasa kan ma'adinai.

Bisa ga wannan sabon kundin dokar man fetur da aka cimma, kashi 15 cikin 100 na kudaden da ake samu da suka hada da ribar da ake samu daga ciniki da haraji, za'a tura su ga hukumomin jihar da gundumomi na yankin Diffa dake kuriyar gabashin kasar da wannan aikin harakar man fetur ya shafa.

A cewar gwamnatin kasar Nijar, mataki ne na yin adalci ga wadannan yankuna, musammun a gundumomin da ake samun kamfanonin dake hakar albarkatun ma'adinai da na man fetur dalilin illa da wadannan kamfanoni suke janyowa ga lafiyar al'umma da muhalli. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China