in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaro ta ko ta kwana ta Sudan ta yi bore a yammacin Darfur
2013-04-22 09:54:47 cri

Wassu gungun rundunar tsaro ta ko ta kwana karkashin gwamnatin kasar Sudan a yammacin yankin Darfur a jiya Lahadi 21 ga wata suka yi wani bore daga sansaninsu dauke da makamai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar SUNA ta ba da labari.

Rundunar dake jibge a Genina na yammacin Darfur, sun wawushe kayayyakin aiki da na abinci, in ji rahoton.

Gungun rundunar sun bude wuta suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi a cikin gari, suka tsorata mazauna wurin kafin sun gangara su wuce zuwa kudu maso yammacin garin ba tare da jikkata ko hallaka wani ba, a cikin bayanin da ma'aikatar harkokin cikin gida ta fitar ma SUNA.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China