Wani shaci a cikin kundin tsarin mulkin kasar da ya rage wa'adin shugaban kasa kuma ya kare 'yancin yawancin al'umman kasar ya samu amincewa daga mafi rinjayen wadanda suka kada kuri'unsu na raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana a ranar Talatan nan.
Aiwatar da wannan kundin tsarin mulkin bisa doka wanda har ila yau zai bukaci amincewar majalissar dokokin kasar zai share fage ga babban zaben kasar da za'a yi a wannan shekarar, da ake ganin zai zama wata babbar gwagwarmaya tsakanin shugaban da ya dade a kan karagar mulkin kasar Robert Mugabe na jam'iyyar ZANU-PF tare da babban 'dan hamayya da shi kuma firaminista Morgan Tsvangirai na jam'iyyar MDC-T, abin da zai kawo karshen wa'adin shekaru hudu da aka yi ana mulkin zaman doya da manja.
Lovemore Sekeramyi, babban jami'in zaben kasar ya shaida ma manema labarai a Harare, babban birnin kasar a ranar Talata cewa, wannan kundin tsarin mulkin da aka tsara ya samu amincewar al'ummar kasar fiye da miliyan uku kuma kasa da 180,000 ne kawai suka ki amincewa da shi.
Hukumar zaben kasar tun da farko ta sanar da cewa, mutane kusan miliyan 6 ne suka yi rajistan kada wannan kuri'ar raba gardama.(Fatimah)