A ranar 15 ga wata, kwamitin sulhu na M.D.D. ya ba da sanarwa cewa, dakarun dauke da makamai da ke adawa da gwamnatin na Al-shabaab sun dauki alharin kai hare-haren ta'addanci, kuma kwamitin sulhu na M.D.D. ya yi Allah wadai da wannan lamari da kakkausan harshe.
Kwamitin sulhu na M.D.D. ya sake nanata cewa, duk ayyukan ta'addanci, laifuffuka ne da za a hukunta wa, haka kuma ya sake jaddada cewa, kwamitin sulhu na M.D.D. yana shirin daukar matakai game da wadannan mutane da suka kawo kalubale game da zaman lafiya da karko a kasar Somaliya, sannan kuma ya nuna goyon baya game da yunkurin samar da zaman lafiya da sulhu a kasar Somaliya.
Ban da wannan kuma, a ranar 15 ga wata, sakatare janar na M.D.D. Ban ki-moon ya ba da wata sanarwa, inda ya ce, ya ba da tabbaci cewa, wadannan aika-aikar ba za su kawo sauyi ga niyyar jama'ar Somaliya ta neman samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Somaliya ba.(Bako)