Tawagar sa ido kan zaben raba gardama da aka gudanar a kasar Zimbabwe, ta kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC, ta amince da yadda wannan zabe ya gudana cikin managarcin yanayi. Jagoran tawagar kuma ministan harkokin wajen kasar Tanzania Bernard Membe ne ya bayyana hakan ga manema labaru, yana mai cewa, an gudanar da zaben lami lafiya, ba kuma tare da wani korafi na magudi ba.
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai al'ummar kasar ta Zimbabwe suka kada kuri'unsu, kan batun amincewa da daftarin kundin dokokin kasar, wanda tuni ake hasashen zai samu amincewa da gagarumin rinjaye, ganin yadda manyan jam'iyyun kasar suka nuna goyon bayansu gare shi, kafin kada kuri'un al'ummar kasar.(Saminu)