in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kungiyoyi masu makamai a gabashin DRC da su ajiye makamai
2013-05-17 11:03:55 cri

An bukaci gungun kungiyoyi masu makamai da ke gabashin DRC-Congo da su dauki niyyar ajiye makamai bisa ra'ayin kansu kafin tura rukunin sojojin MDD, in ji mista Lambert Mende, kakakin gwamnatin Congo a yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar 16 ga watan Mayun shekarar 2013 a birnin Kinshasa.

'Abu mafi kyau shi ne su ajiye makamai bisa kashin kansu, in ba haka ba, a shirye muke mu yi amfani da karfin damtse.' a cewar mista Menda tare da jaddada cewa, lokaci kadan ne ya rage gare su.

Kasar DRC-Congo ta bukace su da su ajiye makamai domin su nemi a saurare su ta wata hanya, amma ba tare da makamai ba, gwamnati ta ba su dogon lokaci domin su yanke shawara, in ji mista Mende.

Haka kuma wannan jami'i ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa na bukatar a warware rikicin gabashin kasar ta hanyar siyasa, domin yin amfani da karfin soja bai zama wajibi ba, ana sa ran warware wannan matsala cikin ruwan sanyi ba tare da an kashe wani 'dan kasar Congo ba.

Ban Ki-moon, babban sakatare janar na MDD zai kai ziyarar aiki a ranar 22 ga watan Mayu a kasar ta DRC-Congo da ta shafi batun shirin tura sojojin MDD. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China