Kungiyar 'yan tawayen M23 ta bukaci tsagaita bude wuta kafin komawa teburin shawarwarin zaman lafiya tare da gwamnatin jamhuriyar demokadiyyar Congo DRC a birnin Kampala, in ji sabon shugaban 'yan tawayen M23, Bertrand Bisimwa a ranar Alhamis.
'Muna shirin komawa teburin shawarwarin zaman lafiya na Kampala, idan har gwamnatin Kinshasa ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da mu.' in ji mista Bisimwa, tare kuma da bayyana cewa, mun lura da rundunar sojojin gwamnatin Kinshasa na samun dauki daga wasu munanan dakarun da suka hada da wasu dakarun FDLR na kasar Ruwanda. (Maman Ada)