Wani dauki ba dadi da ya auku a gabashin DRC wato jamhuriyar dimokuradiyyar Congo, tsakanin dakarun 'yan tawaye da na sojojin gwamnati, ya sabbaba rasuwar farar hula guda 1, yayin da kuma wani jami'in aikin wanzar da zaman lafiya na MDD, da wasu mutane 19 suka samu raunuka.
Yayin taron ganawa da 'yan jaridu na rana rana da ya gudana ranar Laraba 27 ga watan nan, mataimakin kakakin MDD Eduardo Del-Buey, ya bayyana cewa, fadan ya barke ne a sansanin rundunar sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD wato (MONUSCO), wanda ke Kitchanga a arewacin Kivu, inda dakarun 'yan tada kayar baya na APCLS,suka kafsa fada da sojojin gwamnati.
A halin da ake ciki dai, ana fama da yanayin rashin tabbas a wannan yanki, inda rundunar samar da zaman lafiyar ke ba da kariya ga kimanin farar hula da yawansu ya kai 400 a wannan sansani na Kitchanga.
Wannan yanki na gabashin jamhuriyar dimokuradiyyar Congo dai, na shan fama da rikice-rikice tsakanin dakaru masu dauke da makamai cikin 'yan watannnin nan, tun bayan da sabuwar kungiyar nan ta M23 ta fara gudanar da hare-hare a yankin arewacin Kivu a farkon shekarar da ta gabata. Kafin kuma a shawo kan lamarin a shekarar ta bara, sai da wannan kungiya ta kwace babban birnin lardin arewacin Kivu wato Gao.
Tashe-tashen hankula a wannan yanki dai kawo yanzu sun sanya kimanin mutane dubu 475 rasa matsugunnansu, baya ga sama da mutane dubu 75 da suka yi gudun hijira, zuwa makwaftan kasashen Ruwanda da Uganda.(Saminu)