Hong Lei ya bayyana cewa, kasar Sin ta sa lura sosai kan halin da ake ciki a kasar Lebanon, kana tana fatan bangarori daban daban da abin ya shafa da su hada kai da yin hakuri da kwantar da hankali, da ci gaba da yin shawarwari don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, wani bom da aka dasa a cikin wata mota ya fashe a birnin Beirut na kasar Lebanon a ranar 19 ga wata, wadda ta haddasa mutuwar mutane 8, ciki har da shugaban hukumar leken asiri ta kasar Wissam al-Hassan. (Zainab)