Wani rikici ya barke tsakanin masu dauke da makamai dake goyon bayan gwamnatin kasar Sham da dakarun darikar Sunni, dake marawa kungiyar adawa da gwamnatin baya, a karkarar Tripoli, dake arewacin kasar Lebanon. Fadan da aka shafe kwanaki shida ana yin sa, ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 18, yayin da wasu 100 kuma suka samu raunuka.
Rundunar sojojin kasar ta Lebanon sun ci gaba da tura karin dakaru zuwa wannan yanki, an kuma kafa karin tasoshin bincike, tare da mayar da martani ga harin da aka kai musu.
Bisa sanarwar da ofishin shugaban kasar Lebanon ya bayar, an ce, shugaban kasar Michel Suleiman, ya jagoranci wani taron kwamitin tsaron kasar a ranar 9 ga wata, inda ya saurari rahoton da kwamandan kasar ya bayar don gane da halin da ake ciki, tare kuma da tattaunawa kai tsaye, da tsai da wata muhimmiyar manufa a gwamnatance, domin dakatar da rikicin dake abkuwa tsakanin bangarori daban-daban a kasar, tare kuma da farfado da doka da oda a biranenta, sai dai kawo yanzu, ba a zayyana hakikanin abubuwa dake kunshe cikin wannan manufa ba. (Amina)