in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashewar bom a Beirut ta kashe mutane 8
2012-10-20 17:33:58 cri
An samu fashewar wani bom da aka dana cikin mota a birnin Beirut, fadar mulkin kasar Lebanon, a ranar Jumma'a 19 ga wata, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 8, ciki har da wani babban jami'in hukumar leken asirin kasar, Wissam El Hassan, tare da raunata jama'a fiye da 80. Bayan abkuwar lamarin, ministan labaru na kasar, Omran al-Zohbi, ya bayyana cewa wannan lamari 'harin ta'addanci ne na rashin imani'. A halin yanzu ana gudanar da bincike kan wannan lamarin yadda ya kamata.

A nasa bangare, shugaban kasar Lebanon, Michel Suleiman a cikin jawabinsa kan wannan hari ya yi kira ga jama'ar kasar da su zama tsintsiya madaurinki daya tare da sanya muhimmanci kan tsaron al'umma da moriyar kasa, da kokarin dakile makarkashiyar sanya jama'ar kasar zub da jini sakamakon ja-in-ja da bangarorin dake waje da kasar suke yi. Ban da haka, Najib Miqati, firaministan kasar shi ma ya bayyana cewa, hukumar kasar za ta tantance wadanda suke da hannu kan wannan danyen aikin, kuma za a gurfanar da da su gaban kotu.

A wannan rana kuma, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya nuna takaicinsa kan wannan hari ta bakin kakakinsa. Haka kuma ya bukaci a yi cikakken bincike kan lamarin domin cafke wadanda suka aikata shi. Sa'an nan kwamitin sulhu na MDD da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa su ma sun la'anci farmakin. A nata bangare kuma, mai magana da yawun majalisar gudanarwar kasar Amurka, Victoria Nuland, ita ma ta yi Allah wadai da farmakin, tare da bayyana shi a matsayin aikin ta'addanci. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China